7 Yuli 2025 - 22:21
Source: ABNA24
Yamen: Ta Harba Makamai Masu Linzami Kan Cibiyoyin Isra’ila Martani Ga Harin Da Isra’ial ta Kai Ma Ta

Yaman ta mayar da martani ga hare-haren ta hanyar harba makamai masu linzami 11 da jirage marasa matuka a cibiyoyi masu mahimmanci na Isra'ila, ciki har da filin jirgin sama na Ben Gurion da tashar Ashdod

Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (A.S.) – ABNA – ya habarta cewa: Kakakin rundunar sojin Yaman a cikin wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, dakarun tsaron saman kasar sun yi nasarar mayar da martani kan hare-haren da Isra'ila ta kai kan wasu garuruwan kasar ta Yemen, kuma a matsayin martani ga wadannan hare-hare, kasar Yemen ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami 11 da jirage marasa matuka a wasu muhimman cibiyoyi na Isra'ila da suka hada da tashar jirgin saman Ben Gurion da tashar jiragen ruwa ta Ashdod. Dukkan makamai masu linzami da jirage marasa matuka sun yi nasarar kai hari a wurarensu. Ya kara da cewa: Mun kuduri aniyar ci gaba da kewanyar teku a kan Isra'ila.

Sannan kamfanin jiragen ruwa na Birtaniya Merchant Marine ya sanar da faruwar wani sabon hari da ya shafi wani jirgin ruwa mai nisan mil 49 kudu maso yammacin Hodeidah na kasar Yemen a cikin tekun Bahar Maliya.

Birgediya Janar Yahya Sare: Cikin Ikon Allah Jirgin Ruwa Na Magic Seas Ya Nutse A Tekun Bayan Da Sojojin Mu Suka Kai Masa Hari.

Wannan aiki ya kasance martani ne ga saba ka'idojin da kamfanin kera jiragen ruwa ya yi, wanda ya sha shiga tashoshin jiragen ruwa na yankunan Falasdinawa da aaka mamaye. A karshen wannan cin zarafi, jiragen ruwa guda uku na wannan kamfani sun shiga tashoshin ruwan yankunan da aka mamaye a makon da ya gabata, duk da gargadin da sojojin ruwan mu suka yi.

Ansarullah Yemen: Sun Tabbatar Da Kwarewa Da Jajircewar Nau’rorin Tsaron Samansu Na Kariya

Hussein al-Azzi memba na majalisar siyasa ta Ansarullah ya sanar da gagarumin nasarar da sojojin tsaron saman Yamen suka samu wajen tunkarar harin da yahudawan sahyuniya suka kai lardin Hodeidah, yana mai bayyana wannan aiki a matsayin "babban kwarewa".

Al-Azzi ya rubuta a cikin wani sako a kafar sadarwa ta X cewa: Dukkanin abubuwan fasaha na wannan aikin an rubuta su ta hanyar kwararrun da suka dace kuma za a yi amfani da su a matsayin tushe don sababbin ci gaba, kamar kullum. Ya jaddada cewa wannan lamari ne mai matukar muhimmanci.

Ya kuma yi nuni da cewa wadannan hare-haren na iya zama mafarin tabrbarewar rikicin da za’a dade ana fama da shi, inda ya kara da cewa: "labarunrukan hangen nesa sun nuna cewa halakar yahudawan sahyoniya zai kasance a hannunku insha Allah."

Wadannan kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron sararin samaniyar kasar Yemen suka kame tare da dakile wasu hare-haren makiya a sararin samaniyar kasar ta Yemen a 'yan kwanakin nan.

Kafofin yada labarai na Yamma sun tabbatar da nutsewar jirgin ruwan Magic Seas bayan harin da Yemen ta kai masa

Rundunar Sojin Yaman ta jaddada cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da karfin da ya dace wajen dakile duk wani jirgin ruwa na wannan kamfani da ke hada kai da makiya yahudawan sahyoniya tare da keta dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye. An kuma jaddada cewa, jiragen ruwan wannan kamfani za su zama halaltaccen hadafi ga sojojin kasar Yamen a duk inda suke, kuma duk wani nauyi ya rataya a wuyansu. An bayar da gargadin ne gwargwadon yadda doka ta tanada.

Your Comment

You are replying to: .
captcha